Wani Mutum Ya kai ƙarar Hadiza Gabon Saboda Ta ƙi Auransa

0
166

Wani ma’aikacin gwamnati Bala Musa mai shekaru 48 a duniya a ranar Litinin ya maka wata jarumar fina-finan Kannywood Hadiza Gabon a gaban kotun shari’a da ke Kaduna saboda ta ki aurensa.

Wanda ya shigar da karar ya shaidawa kotu cewa yana da alaka da jarumar kuma ta yi alkawarin aurensa.

Musa ya shaida wa kotun cewa, “Ya zuwa yanzu na kashe mata N396,000. Duk lokacin da ta nemi kudi ina ba ta ba tare da bata lokaci ba tare da fatan za mu yi aure.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa an fara sauraren karar ne a ranar 23 ga watan Mayu, amma Hadiza ba ta kotu.

Lauya wanda a ke kara Kabir ya roki kotun da ta kara masa lokaci domin gabatar da wanda yake karewa a kotu.

Khadi, Malam Rilwanu Kyaudai, ya dage zaman zuwa ranar 13 ga watan Yuni.