NNPC ya nemi afuwan ‘yan Najeriya kan karancin man fetur

0
52

Shugaban Kamfanin mai na kasa, NNPC ya bai wa ‘yan Najeriya hakuri kan matsin da suka sake tsintar kansu sakamakon karancin man fetur.

Shugaban kamfanin man, Mele Kolo Kyari ya tabbatar wa manema labarai cewa ana sa ran matsalar ta yanke cikin ƴan kwanaki kaɗan masu zuwa.

Kalaman Mele Kyari na zuwa ne a daidai lokacin da al’umma ke ci gaba da fuskantar dogayen layukan mai, musamman a manyan biranen ƙasar.

Matsalar ta man fetur, wadda ta ƙi ci ta ƙi cinyewa tun a shekarar da ta gabata, na ci gaba da jefa al’ummacikin garari, yayin da babban zaɓen ƙasa ke ƙaratowa.

Sai dai Mele Kyari ya ce cikin kwanaki biyu masu zuwa za a samu sauki ko da wahalar bata kare ba baki ɗaya domin hukumomi sun ɗauki matakan da suka dace domin ganin an shawo kan matsalar.