Gwamnoni shida sun gaza cin zabe don tsallakawa majalisar dattawa

0
83

Akalla gwamnoni shida masu barin gado sun gaza a yunkurinsu na tsallakawa majalisar dattawan Najeriya bayan wa’adinsu biyu na shekara takwas.
Gwamnonin da ke barin gado sun sha kaye a zaben ‘yan majalisar dokokin kasa da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu a mazabunsu na majalisar dattawa.
Tun bayan da Najeriya ta koma kan turbar dimokuradiyya a shekarar 1999 bayan mulkin soja na tsawon shekaru, majalisar dokokin dattawa na zama a matsayin ‘gidan ritaya’ na tsaffin gwamnoni.
Gwamnonin da suka yi rashin nasara kawo yanzu sun hada da Ben Ayade (Cross River), Samuel Ortom na jihar Benue, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu, Darius Ishaku na Taraba, Simon Lalong (Plateau), Okezie Ikpeazu (Abia) da Atiku Bagudu na Kebbi.
Gwamna Dave Umahi na Jihar Ebonyi da Gwamna Abubakar Bello, na Jihar Neja duk sun samu kujerunsu a Majalisar Dattawa.
A yanzu a na dakon sakamakon gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwa wanda shima ya tsaya zaben sanata bayan da ya ke shirin kare wa’adin sa na biyu a mulki.