An yi garkuwa da dalibai mata biyar a jami’ar tarayya ta Dutsinma

0
82

Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki a dakunan kwanan dalibai na jami’ar tarayya da ke Dutsinma (FUDMA), jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da dalibai mata guda biyar.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar yau  Laraba, a dakunan kwanan dalibai da ke a Dutsinma.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wani bayani dangane da halin da wadanda abin ya shafa ke ciki domin wadanda suka yi garkuwa da su ba su tuntubi iyalansu ba.

Shugaban sashin hulda da jama’a na jami’ar Habibu Umar Aminu ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe biyu na safiyar ranar Laraba, inda ya kara da cewa ana ci gaba da kokarin kubutar da wadanda lamarin ya shafa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, ASP Sadiq Aliyu Abubakar, ya ce an kama mutum daya da ake zargi da bayar da bayanai ga ‘yan ta’addan.

Ya bayyana cewa an kuma kama wasu mutane da ake zargin suna da hannu wajen yin garkuwa da daliban.