Babu wata tattaunawa tsakanin Kwankwaso da Atiku-NNPP

0
43

Jam’iyyar NNPP ta ce babu wata tattaunawa tsakanin dan takararta na shugaban ƙasa, Injiniya Rabi’u Musa Kawankwaso da takwaransa na PDP Atiku Abubakar.

A wata hira da BBC, Atiku Abubakar, ya yi iƙirarin cewa suna magana da wasu jam’iyyun adawa don haɗa-gwiwa su ƙwace mulki daga jam’iyyar APC mai mulkin kasar.

Shugaban jam’iyyar NNPP ta ƙasa, Farfesa Rufai Alƙali, ya shaida wa BBC cewa babu wata magana mai kama da haka sam.

Ya ce, “Mu gaskiya ba mu san wannan magana ba haka kuma ba mu san inda ta samo asali ba, mutanenmu sun fusata matuka saboda an sha wahala wajen gina wannan jam’iyya ta mu ta NNPP.”

Ba ma bacci ba ma hutawa muna neman yadda zamu ceto kasarmu, a yanzu jam’iyyarmu na kara samun farin jini da karbuwa a wajen jama’a, in ji shi.

DAGA BBC