Ta yaya sayar wa Dangote ɗanyen mai a naira zai taimaka wa Najeriya?

0
4

A ranar Litinin majalisar ministoci ta Najeriya ta bayar da umarnin a riƙa sayar da ɗanyen mai ga matatun mai na cikin gida a kuɗin ƙasar na naira.

A zaman majalisar na ranar Litinin da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta, an buƙaci matatun man da ke ƙasar su sayar da man da aka tace a naira.

Kazalika, an umarci kamfanin mai na ƙasar NNPCL da ya tattauna da matatar man Dangote da sauran matatun mai na cikin gida da nufin kawo ƙarshen takun-sakar da ke tsakaninsu game da sayar da ɗanyen man.

Tuni dai masana suka fara tsokaci a kan gagarumin yunƙurin na daidaita farashin man fetur, da kuma farashin dala da naira da gwamnatin Najeriya ke son yi.

Sabuwar dabarar, a cewar masana, na nufin kawar da buƙatu masu sarƙaƙiya a cinikayya da ƙasashen waje da ta haɗa da musayar kuɗi, yayin da sabuwar hanyar tace man a cikin gida za ta zo da sauƙi da kuma bunƙasa tattalin arziki da masana’antu, tare da zawarcin masu zuba jari daga ƙasashen ƙetare.

Yunƙurin da Najeriya ta yi na sayar da ɗanyen mai ga Dangote a naira ya janyo hankalin ƙasashe a kasuwannin matatun man fetur da iskar gas na duniya.

Manazarta sun lura cewa matakin na nuna gagarumin sauyi ga manufofin makamashin Najeriya da fifita tace ɗanyen man a cikin gida maimakon fitar da shi waje a tace sannan a mayar da shi cikin gida.