Akwai masu yi wa Tinubu zagonkasa a fadar shugaban kasa

0
72

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi zargin cewa akwai wasu mutane a fadar shugaban kasa da ke yin zagonkasa wa Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Ya yi wannan zargin ne a lokacin da yake magana a shirin “Sunrise Daily’, shirin karin kumallo na gidan talabijin na Channels.

Elrufa’í, ya ce mutanen, da bai bayyana sunayensu ba sun ji haushin yadda Tinubu ya doke dan takararsu a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC.

Ya ce mutanen suna fakewa da burin shugaban kasa Muhammadu Buhari na yin abin da yake so.

Gwamnan ya kuma ce duk da mahimmancin sake fasalin takardar kudin Naira yin ta a wannan lokaci a cikin wa’adin da aka bayar bai da wani tasiri a siyasa ko tattalin arziki.

Kalaman El-Rufai na zuwa ne mako guda bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyya mai mulki ya ce akwai shirye-shiryen hana shi cin zabe.

Tinubu ya ce karancin man fetir da sake fasalin kudin Naira a na yi ne domin hana shi cin zabe.