Hukumar tsaro ta DSS ta damke masu sayar da sabbin kudi

0
82

Hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS, ta sanar da kama wasu da a ka zarga aikata laifukan sayar da sababbin takardun kudin da gwamnati ta fitar a sassan Najeriya.

Wannan na cikin wata sanarwa da hukumar tsaron ta fitar ta hannun kakakinta Peter Afunanya a ranar Litinin a Abuja babban birnin kasar.

Ya ce jami’an hukumar ne suka damke gungun masu aikata laifin yayin da suke tsakiyar hada-hada.

Ya kuma ce, binciken su ya nuna cewa wasu jami’an bankunan kasuwanci na taimaka wa masu aikata wannan zagon kasar da ake wa tattalin arziki.

Hukumar ta gargadi al’umma da su taimaka wa jami’anta da bayanan dukkan wuraren da suka san ana yin wannan haramtaccen cinikin.