Kotu Ta Kori karar Neman Hana Inuwa Takarar Gwaman Gombe

0
37

Kotu Ta Kori karar Da Ke Neman Hana Inuwa Takarar Gwaman Gombe

A jiya ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da a ka shigar gabanta inda a ke bukatar ta hana gwamna Mohammed Inuwa Yahaya takara jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Gombe da ke tafe.

Mai shari’a Binta Nyako, yayin da take yanke hukunci, ta yi watsi da zargin da ake yi wa gwamnan na mika bayanan karya ga hukumar zabe mai zaman kanta.

Jam’iyyar adawa PDP da wasu jiga-jiganta biyu a jihar, Muhammed Jibrin Barde da Timothy Danlele ne suka gabatar da karar a gaban kotun.

Musamman, Barde da Danlele, ta bakin lauyansu, Johnson Usman, sun yi zargin cewa gwamnan ya yi karya a cikin takardun da ya gabatar a gaban INEC.

Sun ce gwamnan bai gabatar da bayanan Gaskiya ba don haka ya kamata a kore shi daga shiga zaben gwamnan da za a yi a ranar 11 ga watan Maris.

Sai dai kotun ta yi watsi da karar bisa rashin cancanta.