Kotu koli ta tabbatar da zaben shugaban kasa Tinubu

0
67
A yau Alhamis ne kotun koli ta tabbatar da nasarar da shugaba Bola Tinubu ya samu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Kotun kolin a hukuncin da ta yanke ta yi watsi da karar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da takwaransa na jam’iyyar Labour (LP) Peter Obi suka shigar. Alkalai bakwai sun yanke hukuncin cewa babu cancantar ‘yan adawar sun daukaka kara kan zargin magudi, karya dokar zabe, da rashin cancantar Tinubu na tsayawa takarar shugaban kasa.
Kotun kolin ta yi fatali da dukkan dalilan daukaka karar Atiku da PDP kan cancanta, rashin bin dokar zabe, kuri’u 25% a babban birnin tarayya Abuja, da kuma magudin zabe
Kotun ta kuma ki karban sabbin shaidun da Atiku ya gabatar kan zargin Tinubu da mallakar shaidar karatu a jami’ar Jihar Chicago na bogi.