Yan sanda a Gombe na binciken wadanda su ka wa yar shekara 58 yankan Rago

0
87

Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe, ta kaddamar da bincike kan mumunan kisan da aka yi wa wata mata ‘yar shekara 58, Aishatu Abdullahi.
Mataimakiyar kwamishinan ‘yan sanda mai kula da sashen ayyuka na rundunar, Hayatu Usman, a madadin kwamishinnan ‘yan sandan jihar Gombe, ya umurci mataimakin kwamishina mai kula da sashin binciken manyan laufuka da ya jagoranci gudanar da bincike kan kisan.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mahid Muazu Abubakar, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce wadanda suka aikata laifin sun kai farmaki gidan Aishatu Abdullahi da ke unguwar jeka da fari a cikin garin Gombe da misalin karfe 9:45 na yammacin ranar Juma’a, inda suka yanka ta kafin su gudu da wayar ta ta hannu.
Rundunar ‘yan sandan ta bayyana kaduwarta da kadua dangane da danyen aikin kuma ta yi alkawarin yin duk mai yiwuwa wajen ganin an hukunta wadanda suka aikata wannan aika-aika.
Ta kuma tabbatar wa da jama’a cewa tana yin duk mai yiwuwa don kamo wadanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kuliya.
Kazalika, cikin wata sanarwa gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya yi allawadai da kisan, inda ya mika ta’aziya ga iyalan marigayiyar, ya bukaci jami’an tsaro su kaddamar da bicike domin gano tare da hukunata wadean da su ka aikta kisan