Kotun koli za ta yanke hukunci kan zaben Tinubu gobe Alhamis

0
81

 

 

A gobe  Alhamis, 26 ga Oktoba, 2023 ne dai kotun kolin za ta yanke hukunci kan shari’ar jam’iyyar Labour da dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi; da Jam’iyyar PDP da dan takararta, Atiku Abubakar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takararta, Bola Tinubu.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da takwaransa na jam’iyyar LP sun shigar da kara suna kalubalantar hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta yanke a ranar 6 ga watan Satumba wanda ya tabbatar da nasarar da Tinubu ya samu a zaben.

Dukkan bangarorin da abin ya shafa sun tabbatar da ranar yanke hukuncin a yau Laraba.

A zamanta na karshe a ranar Litinin, kotun kolin ta kebe sanya rana da za ta yi hukuncin karar da Atiku da PDP suka shigar kan hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta yanke wanda ya tabbatar da nasarar Tinubu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

A ranar Litinin kotun,  karkashin jagorancin alkalai bakwai na kotun bisa jagorancin mai shari’a Inyang Okoro kotun kolin ta bayana cewar za ta sanar da ranar da za a yanke hukuncin.

Kotun kolin ta kuma dauki mahawara daga lauyoyi  kan bukatar da Atiku ya gabatar na kawo sabbin shaidu kan zargin takardun jabu na Shugaban kasa.

Lauyan Atiku Abubakar, Mister Chris Uche, ya bukaci kotun da ta amince da bukatar ta kuma ba da damar daukaka kara, sannan ta haramtawa Tinubu takara.

Lauyan wadanda ake kara, Abubakar Mahmoud na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Wole Olanipekun na Shugaba Tinubu, da Akin Olujinmi na Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun bukaci kotun da ta yi watsi da bukatar da kuma daukaka karar saboda rashin cancanta.