Jami’yar APC ta Dakatar Da Ɗan takarar Gwamna Da Na Sanata A Taraba

0
146

Jam’iyyar APC a jihar Taraba ta kori ɗan takararta na gwamnan jihar a zaɓen 2023 da aka kammala David Sabo Kente kan zargin yi mata zagon- ƙasa.

Kazalika jam’iyyar ta ce ta kori zaɓaɓɓen sanatan Taraba da Kudu David Jimkuta sakamakon zarginsa da ta yi da yi mata zaon-ƙasa a lokacin zaɓukan da suka gabata.

Shugaban jam’iyyar na jihar Elsudi Ibrahim ne ya bayyana a haka a wajen taron manema labarai da ya gudanar a Jalingo babban birnin jihar.

Mista Elsudi ya ce daga yau Sabo Kente ya daina ɗaukar kansa a matsayin mamban jam’iyyar.

Ya kuma jaddada cewa har yanzu shi ne halastaccen shugaban jam’iyyar na jihar, kamar yadda kotu ta tabbatar, bayan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan ƙuri’ar yankan ƙauna da wasu mambobin kwamitin gudanarwar jam’iyyar suka kaɗa masa.