Yan sanda sun ceto mutum biyu da a ka yi garkuwa da su a Gombe

0
36

Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta ce ta ceto wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su a yankin Shabewa da ke karamar hukumar Dukku a jihar Gombe.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ASP Mahid Muazu Abubakar ya fitar Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Gombe.

Sanarwar ta ce rundunar ta samu sahihan bayanan sirri tare da kaddamar da aikin ceto, tare da goyon bayan mambobin kungiyoyin mafarauta da ’yan banga da ke kusa inda aka gano wuraren da ake zargin masu garkuwa da mutanen na fake.

Aikin ceton ya dauki tsawon sa’o’i 48, inda ya a ka yi nasarar ceto mutanen biyu da aka yi garkuwar da su ba tare da biyan kudin fansa ba a safiyar ranar Litinin.

A ranar 8 ga watan Oktoba wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kai farmaki gidan Umar Sambo na yankin Shabewa a Dukku, karamar hukumar Dukku, dauke da bindigogi da wasu muggan makamai.

Sun yi garkuwa da daya daga cikin matansa mai suna Amina Usman Aliyu da dan uwansa Mustapha Sambo.

A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankulansu tare da baiwa hukumomin ‘yan sanda hadin kai ta hanyar samar da bayanai masu amfani don dakile ayyukan miyagun ayyuka a jihar.