Kungiyar Ƴanjarida Ta ƙasa Ta karrama Gwamnan Jihar Kano

0
34

Tawaga daga kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ), karkashin jagorancin shugabanta na kasa, Kwamared Chris Isiguzo, sun karrama gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf

A ranar Lahadi shugabannin kungiyar ta yan jarida sun naɗa Gwamna Abba uban kungiyar.

A jawabinsa gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar wa kungiyar NUJ cewa gwamnatinsa na ci gaba da baiwa kafafen yada labarai goyon baya wajen sauke nauyin da ke kansu.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa na mutunta kafafen yada labarai sosai kuma dangantakarsu da ’yan jarida a Kano da wajenta na da kyau.

Ya yi alkawarin bayar da dukkan goyon bayan da ya dace ga kungiyar da mambobinta.

Credit: Hamada Times