Ba za mu kara wa’adin daina karban tsoffin kudi ba- CBN

0
81

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce ba za a kara wa’adin ranar 31 ga watan Junairun wannan shekara ba domin daina karban tsoffin takardar kudin N200, N500 da N1,000 ba.

Gwamnan babban bankin CBN, Godwin Emefiele ne ya sanar da hakan bayan taron kwamitin kula da harkokin kudi na bankin a Abuja yauTalata.

Babban bankin na CBN ya kuma daga darajar tsarin kudi, wanda ke auna yawan kudin ruwa zuwa kashi 17.5 cikin dari.

A cewarsa, garkuwa da mutane da karbar kudin fansa ya ragu tun bayan da aka sake fasalin takardun kudin.

Ya kuma ce lokacin da aka bayar na musanya tsofaffin takardun kudi na Naira da sababbi ya isa ‘yan Najeriya su rika zuwa bankunan kasuwanci su karbi sabbin takardun kudi.
A ranar 26 ga Oktoba, 2022 ne CBN ya bayyana shirinsa na sake fasalin takardun kudi guda uku.