Zazzabin Lassa Ya kashe Mutum 13 a Jihar Edo.

0
78

Akalla mutum 13 ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu 115 suka harbu da cutar zazzabin Lassa a Jihar Edo.

Kwamishinan Lafiya na Jihar, Farfesa Akoria Obehi, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Benin, babban birnin Jihar.

A cewarsa, gwamnatin jihar ta zage damtse wajen ganin ta dakile yaduwar cutar a fadin jihohin da cutar da barke.

Ya ce sun samu karin mutum takwas da suka kamu da cutar, wanda adadinsu ya kai 115 zuwa yanzu kuma suna Asibitin Koyarwa na Irrua inda suke karbar magani.

Akoria, ya bukaci al’ummar jihar da suka fuskanci matsanancin ciwon kai, zazzabi ko amai, da su garzaya asibitin da ke kusa da su don neman daukin likitoci.

Yanzu haka dai cutar zazzabin Lassa ta bulla a Jihohin Kano da Bauchi da Gombe da Filato da Legas da sauransu.

Sai dai Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka (NCDC), ta ce tana aiki kafada da kafada da gwamnatocin Jihohi don dakile cutar.