An Karrama Dattijo Mai ƙirkire-ƙirƙire Da Bai Yi Boko Ba Da Digirin Digirgir

0
74

Jami’ar jihar Gombe ta ƙarrma dattijon ɗan shekaru 70 Hadi Usman da digirin girmamawa na Dakta.

Jami’ar ta karrama dattijon ne a ranar Asabar yayin bikin yaye ɗaliban jami’ar.

Dattijon wanda bai taɓa karatu a makarantar boko ba yayi fice wajen ƙirkire-ƙirƙire na abubuwan fasaha da su ka haɗa da risho na girki mai amfani da ruwa maimakon man kanazir ko iskar gas.

Dattijon ya halarci bikin baje kolin fasaha na ƙasa da a ka gudanar shekarun baya saboda irin bajintar da ya nuna wajen ƙirkire-ƙirƙire.

Jami’ar jihar Gomben dai da ta karrama wannan dattijon dama ta dauke shi aiki.

Dattijo Hadi dai ya shiga sahun mashahuran mutane da jami’ar ta karrama da su ka haɗa da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima.