Sabon shugaban hukumar lura da aikin hajji na ƙasa ya ziyarci Gwamna Inuwa

0
129

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya karbi bakuncin sabon shugaban hukumar alhazai ta kasa (NAHCON), Alhaji Jalal Ahmad Arabi, a masaukin gwamnan dake Abuja.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Ismail Uba Misilli DG na Yada Labarai na gidan gwamnatin jihar Gombe ya fitar.

Alhaji Jalal Arabi ya samu tsakiyar wasu fitattun mutane, ciki har da mai baiwa shugaban kasa shawara kuma tsohon ministan babban birnin tarayya, Dr. Aliyu Modibbo Umar, da tsohon shugaban NAHCON, Barr. Abdullahi Mukhtar.

Da yake nuna jin dadinsa da irin tarbar da aka yi masa, sabon shugaban hukumar ta NAHCON, ya kuma yaba da goyon baya da kwarin gwiwar da gwamnan ya ba shi dangane da sabon nadin nasa.

Idan za a iya tunawa, a baya Gwamna Inuwa Yahaya, cikin wata sanarwar manema labarai, ya bayyana jin dadinsa da nadin Alhaji Jalal Arabi da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a matsayin shugaban hukumar NAHCON, inda ya yabawa shugaban Najeriya bisa zabo gogaggen masanin aikin gwamanti.

Daga nan sai ya ja hankalin Alhaji Jalal Arabi da ya yi amfani da kwarewarsa da iliminsa wajen farfado da hukumar Hajji ta kasa.