An yankewa likita hukuncin ɗaurin rai-da-rai a kan fyade

0
182

Kotun da ke shari’ar laifukan lalata da cin zarafi a jihar Legas da ke zaune a Ikeja ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai  daraktan kula da lafiya na wani asibin kula da cutar daji, Dokta Olufemi Olaleye, bisa samunsa da laifin lalata da yar’uwar matarsa.

Mai shari’a Rahman Oshodi ya yanke masa hukunci a yau Talata bayan ya same shi da laifin lalata da yarinya ‘yar shekara 15.

Alkalin kotun ya ce masu gabatar da kara sun gabatar da gamsasssun hujjoji, kuma dukkan shaidun da ke gaban kotun sun tabbatar da wanda a ke kara rya aikata laifin.

An gurfanar da Olaleye ne a kan laifuka biyu da suka shafi lalata da kuma cin zarafi ta hanyar saduwa da  ‘yar uwar matarsa,.

An gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kotu tun a ranar 30 ga Nuwamba, 2022, kuma ya musanta aikata laifin.